A ran 31 ga watan nan, babban kwamishinan hukumar 'yan gudun hijira ta M.D.D. Ruud Lubbers ya isa Conakry, babban birnin kasar Guinea domin duba ci gaban da aka samu wajen komar da 'yan gudun hijira bayan da aka kawo karshen yake-yake a wasu kasashen yammacin Afrika.
A wannan rana, Mr. Lubbers da shugaba Lansana Conte na kasar Guinea da jami'an M.D.D. da ke kasar sun yi musayar ra'ayoyinsu kan yadda kasar Guinea za ta karbi wasu 'yan gudun hijira, kuma da yadda za a komar da 'yan gudun hijira na kasashe wadanda suke iyaka da kasar Guineam amma yanzu suke zaune a kasar Guinea. Mr. Lubbers ya kara da cewa, hukumar 'yan gudun hijira ta M.D.D. za ta taimaki gwamnatin Guinea wajen wasu ayyukan yau da kullum a kasar bayan an komar da 'yan gudun hijira daga kasar Guinea. (Sanusi Chen)
|