Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-01 16:35:45    
za a aika da wata kungiyar sulhutawa zuwa kasar Cote dI'voire

cri

Shugaban kasar Cote dI'voire Laurent Gbagbo a ran 31 ga watan Janairu ya tabbatar da cewa, shugaban kasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki zai aika da wata kungiyar sulhutawa zuwa kasar a ran 1 ga watan nan don bayar da taimako ga bangarori daban daban na Cote dI'voire da su sake shimfida zaman lafiya a kasar.

Mr. Gbagbo ya yi wannan bayani ne a ran nan yayin da ya koma birnin Abidjan, babban birnin kasar Cote dI'voire bayan da ya halarci taron shugabannin kawancen kasashen Afirka da aka yi a birnin Abuja, babbar fadar kasar Nijeriya. Kuma ya bayyana cewa, Mr. Mbeki ya riga ya gabatar wa kwamitin sulhu da tsarin zaman lafiya na kawancen kasashen Afirka wata sabuwar shawara kan warware matsalar kasar Cote dI'voire. Haka kuma bisa labarin da muka samu, an ce, kungiyar sulhutawa ta kasar Afirka ta Kudu za ta yi shawarwari tare da tsofaffin dakaru masu yin adawa da gwamnatin kasar Cote dI'voire, kuma za ta gabatar da jadawalin komawar dakarun cikin gwamnatin gamin gambiza ta kasar da kuma na kwance damararsu.(Kande Gao)