Ran 31 ga watan Janairu, a birnin Abuja, fadar mulkin kasar Nijeriya, an rufe taron shugabanni na 4 na kungiyar kawancen kasashen Afirka, wanda aka kwashe kwanaki 2 ana yinsa.
Shugabanni da wakilai na kasashen Afirka 53 da Mista Annan, sakatare-janar na MDD sun halarci taron, inda suka cimma daidaito masu yawa. Shugabanni da wakilai da suka halarci taron sun yi alkawari cewa, za a karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Afirka a fannin tattalin arziki. Har wa yau kuma, sun samu ra'ayi daya kan kafa wani kwamiti na musamman, domin yin bincike kan yadda za a sa kasashen Afrika su kara taka muhimmiyar rawa a wajen MDD. Kuma sun yarda da sa hannu kan yarjejeniyar rashin kai wa juna hari da hada kansu wajen aiwatar da aikin tsaron kasa. Ban da wannan kuma, sun nuna cewa za su yi kokari domin shawon kan bazuwar cutar AIDS da dai sauran ciwace-ciwace a nahiyar Afrika.
Ban da wannan kuma, a gun taron, an yi tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar Kodivuwa, da batun Darfur na kasar Sudan, da dai sauran batutuwa makamantansu. (Bello)
|