shugabannin tsaron kasar Uganda sun isa birnin Kigali, babban birnin kasar Rwanda a ran 31 ga watan nan don yin tattaunawa kan yadda ya kamata a kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Wannan kungiyar shugabannin tsaron kasar Uganda wadda kunshe take da mai rikon mukamin shugaban hukumar leken asiri na soja James Mugira, da shugaban hukumar tsaron kasa wajen harkokin waje Maku Iga da kuma walilin kasar na kwamitin hadin gwiwa na tantancewa da bincike John Kasaija ta gana da Emmanuel ndahiro, babban sakatare na ma'aikatar tsaron kasar Rwanda da kuma walikin kasar Rwanda na kwamitin hadin gwiwa na tantancewa da bincike Hassan Lumumba.
Wanna ne karo na farko da jami'an tsaron kasashen biyu suka yi shawarwari da juna. Kuma kasashen biyu sun kafa kwamitin domin binciken zargin cewa, kasashen biyu suna boye kuma tare da goyon bayan masu tsatsauna ra'ayi na kasashen.(Kande Gao)
|