Labarin da aka kawo mana ya bayyana cewa, a ran 27 ga watan nan da muke ciki, a gun taron tattauna halin mutuntaka na kasashen Afrika da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya shirya, Mr.Jan Egeland mataimakin babban sakatare na majalisar dinkin duniya ya nemi kasashen duniya da su sa lura sosai ga hadarin mutuntaka na kasashen Afrika.
Mr.Egeland ya ce, majalisar dinkin duniya tana tafiyar da aikin ba da taimako a kasar Sudan da Congo Kinshasha da sauran kasashen Afrika cikin dogon lokaci,amma tana gamu da matsalar karancin kudi, ya kamata kasashen duniya sun ba da taimako ga wadannan kasashen dake shan wahalar karancin kudi kamar yadda suka yi kan kasashen dake gabar tekun Indiya.Wato za su ba da taimako ga masu shan wahalar yake yake da yunwa da ciwace ciwace.(Dije)
|