Ran 27 ga wata, wani jami'in MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Liberia ya tabbatar da cewa, a ran 26 ga wata, a birnin Gbarnga da ke arewacin kasar, dakaru masu adawa da gwamnati wadanda aka kwance damararsu sun ta da hargitsi domin nuna kiyayya ga MDD wadda ta kasa biya musu kusi cikin lokaci.
Jami'in ya nuna cewa, wadanda suka ta da hargitsi da ma suna cikin rundunar adawa da gwamnati mai suna 'hadaddiyar kungiyar sulhuntawa da dimukuradiyya ta 'yan Liberia'. A wurin da aka yi hargitsin, an kone kantuna masu yawa, har yanzu ana cikin duhu game da yawan mutanen da suka ji rauni ko mutu. An riga an tura sojojin wanzar da zaman lafiya da 'yan sanda zuwa wurin domin kwantar da kurar da ta tashi. (Bello)
|