Ran 27 ga watan nan, Tony Blaire, firayin ministan kasar Birtaniyya, wanda ke halartar taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin duniya da ake yi a birnin Davos na Switherland, ya yi nuni da cewa, kasar Birtaniyya za ta yi amfani da kafar zaman kasar da ke shugabancin karba-karba ta rukunin kasashe 8, domin neman samun sahihan cigaba wajen kau da talauci a kasashen Afrika.
Mista Blaire ya ce, wahalolin da jama'ar Afirka ke fama da su a cikin zamansu na yau da kullum sun fi tunanin mutane. Shi ya sa, zai yi kokari tare da shugabannin kasashen Afrika domin daukar matakan bayar da taimako ga jama'ar Afrika wajen yakar talauci. Ban da wannan kuma, ya yi nuni da cewa, kasar Birtaniyya za ta kara bayar da kudin Ingila Fam miliyan 25 domin aikin ragakafin cutar malariya a Afrika. (Bello)
|