Ran 27 ga watan, a gun dandalin tattalin arziki da ake yi a birnin Davos na Switherland, an yi tattaunawa kan batun Afrika, masu halartar taron sun yi kira ga kasashen duniya da su mai da hankali kan halin kaka-nika-yi da ake ciki a Afrika, da kuma dauki matakai domin neman kawar da talauci a wurin.
Shugaba Obasanjo na kasar Nijeriya ya nuna cewa, game da kasashen Afrika, samun bunkasuwa ya fi neman taimako muhimmanci. Ya kamata a yi cinikayyar kasa da kasa cikin adalci, ta yadda za a inganta tattalin arzikin kasashen Afrika.
Shugaba Mbeki na kasar Afrika ta Kudu ya yi nuni da cewa, babban aikin kungiyar kawancen kasashen Afrika shi ne tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afrika, domin sai dai a cikin halin lumana ne za a samu bunkasuwa.(Bello)
|