Mai kula da warware matsalar kasar Burundi kuma mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana a ran 26 ga wannan wata cewa, an yi maraba da maido da shawarwari da dakarun adawa da gwamnatin kasar Burundi na kabilar Hutu wato kungiyar 'yantar da al'ummar kasar zai yi tare da gwamnatin kasar, sa'an nan kuma, kungiyar nan ta tsai da kudurin shiga babban zaben shugaban kasar da za a yi bayan watanni da dama.
Mr. Zuma ya yi wannan bayani ne bayan da ya kammala ziyararsa ta yini 2 a kasar Burundi. Ya kara da cewa, yanzu an shiga wani muhimmin mataki a fannin aikin yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar, yana fatan dukan rukunonin kasar za su iya shiga wannan babban zaben kasar.
Ban da wannan kuma, kakakin ofishin shugaban kasar Burundi ya bayyana a ran 25 ga watan nan cewa, gwamnatin kasar ta riga ta yi cudanya da kungiyar 'yantar da al'ummar kasar, bangarorin nan 2 sun yarda da yin shawarwarin zaman lafiya a birnin Dar Es Salaam, babban birnin kasar Tanzania, amma ba a tsai da lokaci ba tukuna.(Tasallah)
|