Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-27 10:38:37    
Majalisar Dinkin Duniya ta nemi hukumar wucin gadi ta kasar Kongo Kinshasha da ta daidaita matsalar rarraba mulki a cikin makon da muke ciki

cri
Labari daga Kamfanin Dillancin Labaru Na Xinhua ya bayyana cewa, a ran 26 ga wannan wata, kakakin rukunin musamman na Majalisar Dinkin Duniya da ke tsugune a kasar Kongo Kinshasha Mamadou Bah ya nemi hukumar wucin gadi ta Kongo Kinshasha da ta daidaita matsalar rarraba mulki na sassan tsaron kai da na gwamnatocin wuri wuri ta yadda za a sake shimfida rundunar soja da kuma kawar da katangar da aka gitta ga babban zabe tun da wurwuri.

A gun taron bayar da labarai, Bah ya karfafa cewa, tattaunawar da za a yi a karshen watan Janairu zuwa farkon watan Fabrairu dangane da ko za a iya tsawaita lokacin wucin gadi ga hukumar wucin gadi ta Kongo Kinshasha wannan dai  ba shawarwarin da za a yi ba ne, wakilan da za su halarci taron dukkansu za su zo daga rukunonin siyasa daban daban.

A gaban zargin da wasu mutanen rukunin siyasa na Kongo Kinshasha suka yi, Bah ya sake jadadda cewa, hakkiin da ke bisa wuyan rukunin musamman na Majalisar Dinkin Duniya da ke tsugunea kasar Kongo Kinshasha shi ne don samar da taimako a fannin fasaha da kudi da guzuri kawai, amma ba zai iya tsai da hakikanin lokacin da za a yi babban zabe a kasar Kongo Kinshasha ba.(Halima)