Ran 26 ga wata, wani jami'in kasar Guinea-Bissau ya tabbatar da cewa, farkon watan mai zuwa, Carlos Gomes Junior, firayin ministan kasar zai kira wani taron kasa da kasa, inda za a bukaci kasashen mahalartar taron da su bayar da taimako ga gwamnatin kasar Guinea-Bissau, yadda za a fid da shi daga cikin mawuyancin hali na rashin kudi.
Bisa labarin da muka samu, za a yi taron a birnin Lisbon, fadar mulkin kasar Potugal. Potugal da Faransa sun nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Guinea-Bissau da ta yi wannan taron.
Bisa bayanin da jami'in ya yi, an ce, a wannan shekarar da muke ciki, gibin kudin da aka samu a cikin kasafin kudin gwamnatin kasar Guinea-Bissau ya kai kudin Amurka miliyan 84. Ban da wannan kuma, kasar tana bukatar kudin taimako dalar miliyan 5, domin shirya babban zaben da za a yi a watan Mayu mai zuwa. (Bello)
|