Alassane Ouattara, shugaban jam'iyyar adawa da gwamnati ta kasar Kodivuwa ya yi nuni da cewa, ya kamata a mika wa MDD ikon shirya babban zaben kasar Kodivuwa da za a yi a watan Oktoba na shekarar nan da muke ciki.
A ran 26 ga wata, a birnin Johannesburg da ke kasar Afrika ta Kudu, Mista Ouattara ya kira wani taron maneman labaru, inda ya bayar da shawarar ga Shugaba Mbeki na kasar Afrika ta Kudu, wanda ke kula da aikin shiga tsakani kan hargitsin da ake yi a Kodivuwa. Mista Mbeki ya ce zai yi la'akari da shawarar da aka ba shi. (Bello)
|