Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-26 10:43:48    
Sojojin Amurka sun girke wani jirgin ruwan yaki a mashigin teku na Guinea

cri

Ran 25 ga wata, wani hafsan sojojin Amurka ya tabbatar da cewa, kasar Amurka ta riga ta girke wani jirgin ruwan yaki a mashigin tekun Guinea da ke yammacin Afirka, domin yin horo kan yaki da ta'addanci da neman wadanda suka fada cikin ruwa da dai sauran batutuwa.

Bisa labarin da muka samu, jirgin ruwan yakin nan da aka girke a mashigin tekun Guinea wani jirgin ruwa ne mai bayar da kayayyaki ga jiragen ruwan yaki da ke tafiya a karkashin ruwa, wanda ke dauke da sojoji 1400. Mai yiwuwa ne zai dade yana aiki a wurin har tsawon watanni.

Wannan hafsan sojojin Amurka ya nuna cewa, Amurka ta riga ta gayyaci Nijeriya da Ghana da dai sauran kasashen da ke kewayen mashigin tekun Guinea da su tura sojojinsu domin shiga rawar dajin. (Bello)