Ran 25 ga watan nan, wata kungiyar agaji da ke kunshe da kwararrun kasar Libiya 17 ta isa birnin Bissau, fadar mulkin kasar Guinea Bissau, domin ba da taimako wajen yaki da farin dango.
Bisa labarin da jami'an kasar Guinea Bissau suka bayar, an ce, kungiyar agajin za ta samar da maganin kashe kwari ton 30 da motocin fesa magani 12 ga kasar Guinea Bissau. Kuma za su aiwatar da aikinsu na kashe farin dango tare da masu aikin agaji da kasar Senegal ta tura su zuwa kasar Guinea Bissau.
Tun daga watan jiya ne, aka samu bullar bala'in farin dango mai tsanani a kasar Guinea Bissau, wanda ya kawo barna ga aikin noma da ake yi a kasar. Kungiyar abinci da aikin gona ta MDD wato FAO ta riga ta bayar da gargadi, cewa mai yiwuwa ne bala'in zai bazu a duk yammacin Afirka. (Bello)
|