A ran 25 ga watan nan, tawagar musamman ta M.D.D. da ke kasar Liberia kan kiyaye zaman lafiya ta tabbatar da cewa, tawagar ta riga ta kara tura sojoji zuwa lardin Maryland da ke kudu maso gabashin Liberia don bayar da taimako kan kwantar da kurar da ta tashi a wurin.
Bisa gabatarwa da wani jami'in kungiyar musamman ya yi mana, an ce, a ran 23 ga watan nan, mazaunan lardin Maryland sun kai farmaki ga wata hukumar 'yan sanda don nuna kiyayyarsu ga gwamnatin wurin da ta saki mutanen da suka yi bikin tunawar matattu ta hanyar yin amfani da kayayyakin jikin 'yan Adam bisa al'adar addini, saboda haka kura ta tashi a wurin. Sai nan da nan gwamnatin wucin gadi na Liberia ta aiwatar da dokar hana fitar dare.(Kande Gao)
|