Jami'an kasashe da shiyyoyi 19 da ke tsakiyar Afirka da gabashinta da wakilan membobin kasashen rukunin kasashe 8 sun yi taro a birnin Dares Salaam, fadar mulkin kasar Tanzania, a ran 25 ga watan, domin kaddamar da shirin raya aikin gona a Afirka, daya daga cikin shirye-shiryen raya Afirka na sabbin abokai, ta yadda za a kara kai yaki ga rashin abinci da yunwa.
Za a shafe kwanaki 4 ana yin wannan taron, babban batun da za a tattauna a kai shi ne yadda za a aiwatar da shirin raya aikin gona yadda ya kamata. (Bello)
|