A ran 25 ga watan, sojojin Sierra Leone sun tabbatar da cewa, an kara karfi wajen tsaron bakin iyakar da ke tsakanin kasar Sierra Leone da kasar Guinea, domin taimaka wa Guinea wajen kama mutanen da ake zarginsu da laifin yunkurin kashe shugaba Lansana Conte na kasar Guinea.
Wani kakakin sojojin Sierra Leone ya bayyana cewa, bisa labarin da aka samu, an ce, wasu 'yan Guinea da ake zarginsu da laifin yunkurin kashe shugaban kasa sun riga sun lababa cikin kasar Sierra Leone, ana fatan jama'ar kasar kada su baiwa wadannan mutane wurin buya. Ban da wannan kuma, ya ce, kasar Guinea ta riga ta tura 'yan sanda na musamman zuwa kasar Sierra Leone, domin kama wadannan mutane. (Bello)
|