Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-21 21:15:39    
Za a hada da tsarin ba da wutar lantarki na kasashen Zambia da Tanzania da Kenya

cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar a ran 21 ga watan nan daga birnin Lusaka, an ce, za a kafa wani tsarin ba da wutar lantarki wanda zai hada da tsarin kasashen Zambia da Tanzania da Kenya. Bayan an kammala wannan tsari, kasar Zambia za ta iya samar da wutar lantarki ga kasashe wadanda suke makwabtaka da ita.

John Wright, shugaban ofishin sa kaimi ga masu zaman kansu da su zuba jari a sha'anin ba da wutar lantarki na kasar Zambia, ya ce, yanzu ba a gama aikin yin kima kan muhalli da zaman al'ummar jama'a a kasar Tanzania ba, an riga an gama dukkan aikin kima a sauran kasashe. Mr. Wright ya ce, za a gama aikin yin kima kan muhalli da zaman al'ummar kasar Tanzania kafin karshen watan Yuli na shekarar nan.

Mr. Wright ya kara da cewa, bayan an gama dukkan aikin kima, kamfanoni masu zaman kansu za su zama muhimman masu zuba jari a wani kamfanin da kasashen Zambia da Tanzania da Kenya za su kafa musamman don ayyukan nan. (Sanusi Chen)