Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-21 20:52:31    
Kasar Afirka ta kudu tana fatan za a kawo masu yawon shakatawa da yawa a kasar

cri
A ran 21 ga watan nan, jaridar Business Day ta kasar Afirka ta Kudu ta tsamo maganar Moeketsi Mosola wanda ke kula da kasuwar yawon shakatawa ta kasar Afirka ta kudu cewar kasar Afirka ta Kudu tana fatan yawan masu yawon shakatawa da za su je kasar Afirka ta kudu a kowace shekara zai kai miliyan 10.5 a cikin shekaru 5 masu zuwa. Yanzu yawan masu yawon shakatawa da suka je kasar Afirka ta kudu ya riga ya kai miliyan 6.5.

Mr. Mosola ya ce, dalilin da ya sa kasar Afirka ta Kudu ta tsara wannan shiri shi ne, asusun kudaden kasa da kasa ya yi hasashen cewa, adadin karuwar tattalin arzikin kasashen duniya zai kai kashi 4.3 cikin dari a shekara mai zuwa. Wannan yana bayyana cewa, mutane da yawa za su iya kashe kudinsu wajen yawon shakatawa. Mr. Mosola ya kara da cewa, bayan sha'anin yawon shakatawa na duniya ya sha wahala sosai a cikin shekaru 3 da suka wuce, yanzu, yana komar da hali yadda ya kamata. (Sanusi Chen)