Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-21 20:38:40    
Dukkan 'yan gudun hijira na Congo Kinshasha da ke Tanzania za su koma gida a shekarar nan

cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar a ran 21 ga watan nan, cewar dukkan 'yan gudun hijira wajen dubu 15 na kasar Congo Kinshasha da ke zaune a kasar Tanzania yanzu za su koma gidajensu kafin karshen shekarar nan. Kwamitin musamman da ke hade da Tanzania da kasar Congo Kinshasha da ofishin babban kwamishina mai kula da harkokin 'yan gudun hijira na M.D.D. ne ya tsara wannan shiri.

Chrysantus Ache, shugaban kungiyar wakilan ofishin babban kwamishina mai kula da harkokin 'yan gudun hijira na M.D.D, ya ce, yanzu ana aiwatar da wannan shirin da ya riga ya zama wani sashe na ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar Congo Kinshasha yadda ya kamata.

A shekarar 2004, an riga an komar da 'yan gudun hijira 2470 na kasar Congo Kinshasha da ke Tanzania gidajensu. (Sanusi Chen)