Bisa labarin da aka samu, an ce, kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa ta riga ta nada Dr. Luis Gomes Sambo, wani tsohon jami'in kasar Angola, direktan ofishin kungiyar da ke Afrika. Dr. Luis Gomes Sambo zai fara wa'azin aikinsa mai tsawo shekaru 5 ne a ran 1 ga watan Fabrairu na shekarar nan.
Kafofin yada labaru na kasar Angola ne suka bayar da wannan labari a ran 21 ga watan nan.
Dr. Sambo, mai shekaru 52 da haihuwa, yana kware kan kiwon lafiyar jama'a. Ya taba hawa kan mukamin mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Angola. Ya kuma taba yin aiki a kasar Guinea Bissau tun daga shekarar 1990 zuwa shekarar 1994 a matsayin wakilin WHO. (Sanusi Chen)
|