Shugaba Obasanjo na kasar Nijeriya ya nuna cewa, gwamnatin kasar za ta yi kokari domin yin amfani da makamashin nukiliya wajen ayyukan kyautata al'umma, kuma ba za ta kera makaman nukiliya masu kare dangi ba.
Ran 18 ga wata, shugaba Obasanjo ya gana da Mista Baradei, shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa, wanda ke ziyara a birnin Abuja, inda ya nuna cewa, gwamnatin kasar Nijeriya tana so ta yi amfani da makamashin nukiliya domin kyautata aikin likita da aikin noma, da kuma yi amfani da ruwa yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, shugaba Obasanjo ya bukaci hukumar da ta bayar da taimako ga Nijeriya wajen horar da kwararrun makamashin nukiliya. (Bello)
|