Bisa shirin da aka tsara, a shekarar 2005, gwamnatin kasar Nijeriya za ta gina hanyoyin mota da tsawonsu zai kai kilomita dubu 5. Adeseye Agunlewe, minista mai kula da ayyukan yau da kullum na kasar Nijeriya ne ya fadi haka a ran 17 ga watan nan.
Ba za ta gina sabbin hanyoyin mota kawai ba, kasar Nijeriya za ta gyara hanyoyin mota da tsawonsu zai kai kilomita dubu 32 a shekarar nan, in ji Ogunlewe.
Mr. Ogunlewe ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, ma'aiktar sha'anin kudi ta riga ta kebe wa ma'aikatarsa Naira biliyan 68 domin gina da kuma gyara hanyoyin mota a cikin shekaru 3 masu zuwa. (Sanusi Chen)
|