Wata kungiyar wakilai ta hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa wadda babban darakta na hukumar El Baradei yake shugabanta za ta kai ziyara na kwanaki hudu a kasar Nijeriya a mako mai zuwa don dudduba wuraren da ake samu tartsatsin nukiliya na kasashen yammacin Afirka.
Bisa labarin da aka samu daga kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, an ce, a cikin ziyararsu, El Baradei da wannan kungiyar wakilai za su yi shawarari tare da shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo da kuma ministocin kasar, kuma za su dudduba wuraren da aka samu tartsatsin nukiliya da kuma kayayyakin nukiliya da ke cikin kasar.(Kande Gao)
|