Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-17 16:09:42    
Shugabannin kasashen Equatorial Guinea da Nijeriya sun tattauna kan maganar raya mashigin teku na Guinea

cri
A ran 16 ga watan nan a birnin Abuja, shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya da takwaransa na kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo wanda ya fara ziyararsa a kasar a wannan rana, sun yi shawarwari kan yadda za a raya yankin mashigin teku na Guinea inda ke cike da man fetur.

A gun shawarwarin da aka shafe awa 1 ana yinsa, shugaba Obasanjo ya nuna farin cikinsa ga hadin guiwar da aka yi ta yi a tsakanin kasashen biyu. Ya kuma ce, wajibi ne kasashen nan biyu su yi kokari tare kan yadda za a sa kwamitin mashigin teku na Guinea ya fara aiki.

A shekarar 1999 ce aka kafa kwamitin mashigin tekun Guinea wanda take hade da kasashen Nijeriya da Sao Tome da Principe da Equatorial Guinea da Gabon da Cameroon da Congo kuma da Angola. Dalilin da ya sa aka kafa wannan kwamiti shi ne kara yin hadin guiwa a tsakaninsu da kuma hana aukuwar tashin hankali a yankin domin maganar man fetur. (Sanusi Chen)