A madadin shugaban kasar Nijeriya kuma shugaban kawancen kasashen Afirka ne, mataimakin shugaban kasar Nijeriya Atiku Abubakar zai tashi daga kasar a ranar Asabar zuwa birnin Nairobi, inda shi da sauran shugabannin kasashen duniya za su hallara a gun bikin sa hannu a kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya ta sa ayar yakin basasa da aka shafe shekaru 21 ana yinsa a tsakanin gwamnati da 'yan tawaye, wato kungiyar 'yantattar da jama'a ta kasar Sudan. Za a yi wannan biki ne a ranar Lahadi, wato ran 9 ga watan nan a Nairobi babban birnin kasar Kenya.
Kamfanin dillanci labaru na Nijeriya ne ya yada wannan labari a ran 6 ga watan nan.
A watan Mayu na shekarar bara, gwamnatin Sudan da 'yan tawayen da ke kudancin kasar sun riga sun kai ga daddale yarjejeniyoyin 6 domin kawo zaman lafiya a tsakaninsu, yarjejeniyoyin sun shafi wasu muhimman matsalolin raba ikon gwamnati da yadda za a yi mulkin yankuna 3 a cikin kwarya-kwaryar tsawon lokaci na shekaru 6 masu zuwa. Ban da wannan, a ran 31 ga watan Disamba na shekarar bara, sun sami ra'ayi daya kan wata muhimmiyar matsala daban da ta kasance a tsakaninsu. (Sanusi Chen)
|