A kwanakin baya ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya aika da wata wasika zuwa ga shugaban kwamitin kawancen kasashen Afirka Alpha Oumar Konare ya ce, kasar Sin za ta gabatar da taimakon kudi na dolar Amurka dubu 400 ga kawancen kasashen Afirka na musamman don aikinsa a yankin Darfur na Sudan.
A cikin wasikar minista Li Zhaoxing ya ce, gwamnatin kasar Sin ta yabawa kokarin da kawancen kasashen Afirka ya yi don warware matsalar Darfur kuma za ta cigaba da goyon bayan aikinsa, tana fata za a daidaita matsalar Darfur bisa shirin kawancen kasashen Afirka. [Musa]
|