Rukunin sojojin injiniyoyi na farko na rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Liberia sun kammala ayyukansu a kasar, kuma a ran 5 ga wata da yamma, sun komo nan kasar Sin. Ta haka, dukan sojojin kiyaye zaman lafiya na rukuni na farko da kasar Sin ta tura zuwa kasar Liberia sun komo kasar Sin.
Bisa abubuwan da aka gabatar, an ce, Majalisar Dinkin Duniya ta ba da lambobin kiyaye zaman lafiya ga dukan sojoji 558 na rukuni na farko na rundunar sojan kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Liberia, wadanda suka hada da sojojin injiniya.(Tasallah)
|