Ran 5 aga watan nan, Ahmed Abul Gheit, ministan harkokin waje na kasar Masar ya bayar da wata sanarwa, inda ya musunta labarin da wasu kamfanonin watsa labaru na kasashen yamma suka bayar wai kasar Masar ta taba yin gwajin makaman nukiliya a cikin asiri bayan ta sa hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
Mista Abul Gheit ya ce, an rubuta labarin ba bisa tushen gasakiya ba, kasar Masar tana bin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya sosai.
Yayin da ake musunta labarin, gwamnatin kasar Masar ta jaddada cewa, ta gudanar da shirinta na nukiliya ne domin bayar da wutar lantarki, ba wai domin kera makmai ba. (Bello)
|