A ran 4 ga watan nan, shugaban kasar Kongo(Kinshasa) Joseph Kabila ya yi gyare-gyare a majalisar ministoci bisa babban mataki, inda ya sallami ministoci da yawansu ya kai 11.
Wadanda aka sallame su sun hada da ministocin tsaron kasa da na tattalin arziki da na ma'adinai da na makamashi da na cinikayya da na zirga-zirga da kuma na ba da ilmi a jami'o'i da dai sauransu. Bisa labarin da muka samu, an ce, wasu daga cikinsu an sallame su ne domin sun yi fakaca da kudin kasa.
Sababbin ministocin tsaron kasa da na tattalin arziki da Mr Kabila ya nada sun zo ne daga dakarun da ba su ga maciji da gwamnatin wato kungiyar "the Congolese Rallay for Democracy".(Danladi)
|