Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-04 20:32:20    
Filin jirgin sama na Lagos zai zama cibiyar sufuri na yammacin Afrika

cri
Hukumomin Kasar Nijeriya na shirin kara kyautata da kuma daukaka filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Lagos cibiyar kasuwanci ta kasar domin ya zama cibiyar sufuri da zirgaga na yammacin Afrika.Kamar dai yadda kamfanin dillancin labarun Nijeriya ya ruwaito.

An ruwaito cewar an ji ministan zirga zirgar jiragen saman kasar Malam Isa Yuguda na cewar, an kara darajar filin jrgin saman Murtala Muhammed dake Ikko ya zuwa cibiyar sufuri a yammacin afrika,don haka muna kokarin yin dukkan abubuwan da suka dace domin cimma wannan buri. Ya kuma cigaba da cewqar a halin da ake ciki ana kan kokarin ganin an kyautata kayayyaki da na'urorin filin jirgin saman domin ya dace da na duniya.

Ministan ya ce ma'aikatar kula da zirga zirgar jiragen saman Nijeriya,a halin yanzu ya dukufa ka'in da na'in wajen ganin an cimma wannan burin ta hanyar mayar da harkokin zirga zirgar jiragen saman Nijeriya da ya zama mafi inganci a nahiyar Afrika, sannan kuma filin jirgin sama na Murtala Muhammed ya zama cibiyar yankin domin a cewarsa kusan kashi 80 cikin dari na yawan zirga zirgar jiragen sama a Nijeriya, daga filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Lagos ne. (Balarabe)