Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Uganda suka bayar a ran 3 ga wata, an ce, Kungiyar kwastam ta Gabashin Afirka ta fara aiki a kasashen Kenya da Tanzania da Uganda tun daga ran 1 ga watan Janairu na shekarar nan, sabo da haka, tun daga watan Fabrairu na shekarar nan ne za a tafiyar da sabuwar manufar harajin kwastam a wadannan kasashe 3. Kwamishina Allen Kagina ta hukumar samun haraji ta kasar Uganda ce ta fadi haka.
Bisa ka'idar da kungiyar kwastam ta gabashin Afirka ta tsara, harajin shiga ko fitar da albarkatun kasa a tsakanin wadannan kasashe 3 zai kai sifiri kawai, amma harajin shiga ko fitar da kayayyakin da aka kusan gama sarrafa su zai kai kashi 10 cikin kashi dari, harajin shiga ko fitar da kayayyakin da aka riga aka gama sarrafa su zai kai kashi 25 ciki kashi dari. (Sanusi Chen)
|