Bisa labarin da aka samu daga jaridar 'The New Vision' ta kasar Uganda a ran 4 ga wannan wata, an ce, ran Lahadi da dare da kuma ran Litinin da safe, mai sulhutawa na kasar Uganda Betty Bigombe da kuma ministan tsaron kasar sun buga wayar tarho ga shugaban 'yan tawaye na kasar Joseph Kony da kuma mataimakinsa Vincent Otti don yin kokari kan sake yin tattaunawa tsakaninsu.
Kuma a ran Litini, yayin da Mr. Bigombe yake zantawa da manema labarai na wannan jarida, ya ce, yanzu ana ta yin kokari don sake fara yin tattaunawa tsakaninsu. Amma ya ki kara yin cikakken bayani a kan wannan.
Amma an ce wai Kony ya yi kukan cewa, gwamantin kasar ba ta da imani, saboda shugaban kasar yana so a kashe shi.(Kande Gao)
|