Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-04 11:00:12    
Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya yi kira ga kawancen kasashen Afirka da ya tabbatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a Sudan

cri
A ran 3 ga wata, shugaban kasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya yi kira ga kawancen kasashen Afirka da ya tabbatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da gwamnatin Sudan da kungiyar 'yantar da jama'ar Sudan wadda ke yin adawa da gwamnati suka kulla a ran 31 ga watan Disamba da ya shige.

A ran nan, Mr.Mbeki ya kammala ziyara ta kwanaki 4 a kasar Sudan. Ya ce, dalilin da ya sa ya jaddada wannan shi ne, sabo da kafin wannan, ba a tabbatar da yarjejeniyar da gwanatin Sudan da kungiyar da ba ta ga maciji da gwamnati da ke kudancin kasar suka kulla ba, wanda kuma ya haifar da ci gaban aukuwar rikici a kasar.

Mr.Mbeki ya kuma taya gwamnatin Sudan da kungiyar da ba ta ga maciji da gwamnati murnar kulla yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a hukunce da za su yi a ran 9 ga wata. Ya ce, Afirka ta kudu za ta yi kokari wajen ba da taimako ga kawancen kasashen Afirka don neman tabbatar da zaman lafiya a Sudan.(Lubabatu)