Ran 28 ga wata, ma'aikatar harkokin gida ta kasar Sudan ta ba da sanarwar cewa, a ran 27 ga wata, sojojin gwamnatin kasar sun murkushe harin da dakarun adawa da gwamnatin kasar suka yi a lardin arewacin Kordofan da ke kasar ta yamma ta tsakiya, inda suka kashe 'yan tawaye 21, kuma suka kwace wasu makamansu.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, wadannan dakarun adawa da gwamnatin kasar sun zo ne daga yankin Darfur na yammacin kasar. Sanarwar nan ta kara da cewa, sojoji 7 na rundunar sojan gwamnatin kasar da 'yan sanda 2 da wasu 'yan rundunar tsaron kai na farar hula sun rasa rayukansu, kuma an rushe wasu gidaje na wurin.
Tun daga watan Fabrairu da ya gabata, dakarun adawa da gwamnatin kasar da ke yankin Darfur sun kai farmaki ne a wannan yanki , inda mutane da yawa suka jikata kuma da dama sun mutu.(Tasallah)
|