Mun sami labari daga kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, kullum kasashen Afrika da kasashen duniya suna ta yin kira kamar haka "Mai da hankali kan Afrika". Yawan mutanen Afrika ya kai kashi 13 cikin dari bisa na dukan duniya, amma jimlar tattalin arzikin nahiyar ya kai kashi 1 cikin dari kawai bisa na duniya, jimlar kudi na ciniki ya kai kashi 2 cikin dari bisa na dukan duniya; a cikin kasashen da suka fi talauci guda 49 na duniya, akwai kasashen Afrika guda 34. Wasu manazarta suna ganin cewa, yanzu wannan babban yankin da ya fi talauci a duniya yana bukatar jawo ainihin hankali daga kasashen duniya.
A cikin tsarin kasuwanci na bai daya na duniya, wasu mutane suna tsammani cewa, Afrika tana fuskantar hadarin da aka riga aka manta da shi, amma idan aka mayar da Afrika bisa matsayin babban yankin da aka manta da shi, wannan bai dace da wasu hakikanin halin da ake ciki ba. Da farko, ko da ya ke ana ta yin yake-yake a kasar Iraqi, kuma rikicin da ke tsakanin kasar Falestinu da kasar Isra'ila ya yi ta tsanani, amma rikici da yake-yaken da ake yi a Afrika sun kai kashi 75 cikin dari bisa na duk duniya, kuma yawan kudin kiyaye zaman lafiya da nahiyar ke samu ya kai kashi 65 cikin dari bisa na dukan duniya, musamman ma hargitsin Darfur ya jawo hankulan dukan kasashen duniya; na biyu, sabo da tsanancewar halin da gabas ta tsakiya ke ciki, da rashin isasshen man fetur, da tashin farashin man fetur a duniya, manyan kamfanonin man fetur na kasashen duniya suna kara zuba jari da habaka harkokinsu a Afrika, Afrika ta riga ta sami muhimmanci a muhimman tsare-tsaren makamashin manyan kasashen da ke yamma; na uku, kamfanin kiyasta muhimman tsare-tsare na kasar Amurka ya bayyana cewa, yanzu, wato lokacin da ake yin aikace-aikacen ta'adanci a dukan duniya, mahukuntan Washington sun fara mai da hankulansu kan babban yankin Afrika bisa ra'ayinsa na tashin hankali.
Ta haka kuma muna iya ganin cewa, Afrika ba ta rasa kula daga kasashen duniya ba, muhimman abubuwa su ne, wane irin kula ya kamata a ba ta, kuma wane irin hanya ce za a zura ido a kai. A farkon shekarar da muke ciki, a lokacin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyara a Afrika ya ce, bisa matsayin kawa, muna mai da hankali kan sha'anin zaman lafiya da bunkasuwa, da sa kaimi ga warware muhimman matsalolin Afrika. Maganar nan da shugaban kasar Sin ya yi ya kawo tasiri sosai a Afrika.
Kan maganar bunkasuwar Afrika da warware matsalar talauci da ciwon Sida a Afrika, manyan kasashen yamma su ma sun taba yin alkawari, amma kadan ne suka tabbatar da wannan.
Girmama hanyar bunkasuwa da jama'ar Afrika suke zabi da kansu, da kiyaye iko da moriya kamar yadda ya kamata na kasashe masu tasowa tare da kasashen Afrika, da nuna goyon baya da juna, da nuna girmamawa da juna, da karanta da juna, da kuma tabbatar da bunkasuwa da wadatuwa tare, su ne muhimman manufar kasar Sin kan Afrika.
Kullum kasar Sin tana sa ido sosai kan Afrika, kuma tana neman bunkasuwar dangantakar da ke tsakaninta da Afrika ta hanyar yin hakikanan aikace-aikace. (Bilkisu)
|