Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-12-27 08:30:50    
Gwamnatin kasar Sudan da kungiyar SPLA za su sa hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya

cri
A ran 24 ga wata, Qutbi al-Mehdi, wato mai ba da shawara kan harkokin siyasa ga shugaban kasar Sudan, ya ce, gwamnati da rundunar soja ta kwatar 'yancin jama'ar Sudan, wato kungiyar SPLA za su sa hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a watan Janairu na shekara mai zuwa a kasar Kenya don sa ayar yakin basasa da aka shafe shekaru 21 ana yinsa a kudancin kasar Sudan.

A 'yan kwanakin nan, mai sulhuntar matsalar Sudan wanda ya zo daga kasar Kenya ya ce, bangarorin nan biyu za su ci gaba da yin shawarwari kan wasu matsalolin da har yanzu ba a warware su ba a cikin lokacin hutu na Christmas domin tabbatar da kai ga daddale wata yarjejeniyar shimfida zaman lafiya kafin ran 31 ga watan da muke ciki. (Sanusi Chen)