Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-12-23 20:14:23    
MDD ta bukaci bangarorin da ke gwagwagwa da juna a Darfur da su yi aiki da alkawuransu

cri
Kakakin babban magatakardan majalisar dunkin duniya a Sudan, Radia Ashuri ta yi kira ga bangarorin da ke kai ruwa rana a yankin Darfur da su mutumta alkawuran da suka domin kare yankin da kuma al'ummarsu.

A wajen wani taron manema labaru da aka shirya a ranar larabannan, Madam Ashur,ta bayyana cewar hakkin kare mutanen yankin Darfur, wani hakki ne da ke rataye a wuyan bangarorin da ke gumurzu da juna a yankin, kuma hakki ne da ke wuyan al'ummar Sudan fiye da sauran masu sa baki cikin lamarin, wato Kungiyar Afirka da kuma Majalisar Dunkin Duniya.

Kakakin ta kuma bayyyana halin tsaro da ake ciki a yankin Darfur da cewar akwai rudarwa kuma mai matukar wahala ne, domin a cewarta har yanzu akan sami y'an matsalolin yin fashi da makami da kuma kai farmaki daga lokaci zuwa lokaci a yankin.

Da take tofa albarkacin bakinta kan tattaunawar baya bayannan da aka yi kan yankin Darfur, tsakanin hukumomin Kasar Sudan da dakarun da ke adawa da gwamnatin ta Sudan a Abuja, sai ta kada baki ta ce, an dakatar da tattaunawar ne domin dukkan bangarorin biyu ba su son cimma wata kwakkwarar yarjejeniya domin warware takaddamr ta Darfur.

Ta ce, kwamitin sulhun Majalisar Dunkin Duniya zai sake amincewa da wani sabon kudurin a kan rikicin yankin Darfur a daidai lokacin da ya dace.(Balarabe)