Ran 21 ga wata gwamnatin kasar Sudan da dakaru masu yin adawa da gwamnatin sun bayar da sanarwar hadin gwiwa, sanarwar ta ce an kammala taron tattaunawar zaman lafiyar Darfur na karo na uku.
Sanarwar ta ce, gwamnatin kasar Sudan da dakaru masu yin adawa da gwamnatin sun riga sun yarda da su tsagaita gaba da juna, kuma za su bi yarjejeniyar tsagaita bude wuta wadda suka yi a watan Afrilu na bana, don haka za su iya sake yi taron tattaunawar zaman lafiya a watan Janairu a shekara mai zuwa.
|