Ran 20 ga wata, jami'an kawancen kasashen Afirka wadanda suke shawo kan matsalar Darfur ta kasar Sudan a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya sun tabbatar da cewa, kawancen ya riga ya ba da umurni ga 'yan kallonsu da su dakatar da aikinsu na sa ido kan tsagaita bude wuta da ake yi a yankin Darfur, don yin binciken lamarin harin da aka kai wa wani jirgin sama mai saukar ungulu na kawancen a wurin.
Jami'an kawancen sun bayyana cewa, a ran 19 ga wata, wannan jirgin sama mai saukar ungulu da ke dauke da 'yan kallo na kawancen ya gamu da harin da aka kai masa daga kasa a kudancin yankin Darfur, amma jirgin saman nan da mutanen da suke ciki ba su ji rauni ba, muhimmin aikin da za a yi shi ne binciko mutanen da suka aikata wannan hari.(Tasallah)
|