Labarin da aka kawo mana ya bayyana cewa,a ran 20 ga watan nan da muke ciki, ma'aikatar tsaron kasar Gambia ta ba da labari cewa, wata rundunar soja dake kunshe da sojoji l96 ta kasar Gambia ta riga ta tashi daga kasar zuwa shiyyar Darfur don shiga aikin duba tsagaita bude wuta.
An ce, tsawon lokacin aiki na wannan rundunar soja zai kai shekara daya a shiyyar Darfur na kasar Sudan.
An kuma bayyana cewa, ana nan ana shirin kara yawan sojoji masu dubawa.(Dije)
|