Yanzu, kasar Sin ta riga ta zama babbar kasa ta biyu mai kashe kudi kan man fetur. Kasar Sin tana bukatar tafiyar da hadin kai sosai da kasashen waje, domin sarrafa man fetur kai tsaye a shiyoyyi masu albarkatun man fetur. Sabo da haka, watakila nahiyar Afrika za ta zama wani sabon abokin hadin kai na kasar Sin kan tsare-tsaren man fetur.
Afrika tana da albarkatun man fetur sosai, kwararu sun kiyasta cewa, har zuwa shekarar 2010, yawan man fetur da za a fitar a kasashen Afrika zai kai kashi 20 cikin dari bisa yawan fitar da man fetur a duka duniya.
Ran 29 ga watan Mayu, maitaimakin shugaban kwamitin raya kasa da gyara kasa na kasar Sin Mr. Zhang Baoguo da ministan ma'adinai da makamashi da man fetur da ruwa na kasar Gabon Mr. Richard Onouviet sun daddale yarjejeniya a birnin Libreville, wato babban birnin kasar Gabon, sun bayyana cewa, bangarorin nan biyu za su yi hadin kai sosai, ba da goyon baya da kwarin gwiwa kan hadin kansu na zuba jari da musayen fasaha a filin ma'adinai da na makamashi, kuma sun karfafa zuciyar masana'antun kasar Sin da su shiga aikin bunkasa albarkatun karfe da ma'adinai.
Ran 20 ga watan Mayu, kamfanin SINOPEC (China Petrochemical Corporation) da kasar Nijerya, wato kasar fitar da man fetur da ta fi girma a Afrika sun daddale yarjejeniya, kungiyar SINOPEC za ta zuba jari dollar Amurka biliyan 0.5 kan nema da habaka man fetur a teku a kasar Nijerya, kuma tun daga watan Yuli na shekarar da muke ciki, za ta shigo da man fetur ganguna dubu 70 daga kasar Nijerya a ko wace rana.
Ran 3 ga watan Feburairu, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya kai ziyara ga kasar Gabon, kamfanin SINOPEC ya sanar da daddale yarjejeniya da kamfani na kasa renon Faransa, karo na farko ne kasar Sin za ta sayi man fetur daga kasar Gabon.
Ran 5 ga watan Feburairu, kamfanin man fetur da gas na kasar Sin ya kuma sanar da cewa, kamfanin nan da kasar Masar da kasar Algeria sun daddale yarjejeniyar hadin kai ta man fetur.
A sa'i daya kuma, ra'ayoyin bainal jama'a na kasashen waje sun mai da hankali sosai kan ziyara da firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao da shugaban kasar Mr. Hu Jintao suka yi a kasashen Afrika daya bayan daya a watan Disamba na shekarar da ta wuce da watan Feburairu a shekarar da muke ciki. Yawancinsu suna ganin cewa, ziyarar da shugabannin kasar Sin suka kai ga kasashen Afrika wannan ya nuna mana cewa, muhimmin abu na shirin tsare-tsare na duniya na kasar Sin shi ne, yi tattaunawa da kasashen Afrika kan kafa hadin kan makamashi, don samun man fetur da gas.
Kan matsalar matsayin man fetur da Afrika ya kai a tsare-tsaren man fetur na kasar Sin, 'dan nazari na cibiyar nazarin matsalolin kasashen duniya na ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mr. Xia Yishan ya ce, "kasar Sin ta riga ta tuna da mai da Afrika zama wata shiyyar bayar da man fetur mai yancin kai." Matsayin da kasashen Afrika suka yi a tsare-tsaren man fetur na kasar Sin yana ta yi muhimmanci.
Kwararun da abin ya shafa sun ba da shawara cewa, shiyyar mashigin teku ta Guinea tana da wadatuwar man fetur, kuma tana da kyakkyawar dangantaka da kasar Sin, sabo da haka, ya kamata kasar Sin ta mai da muhimmanci kan shiyyar mashigin teku ta Guinea da ke yammancin Afrika wajen samun man fetur.
Shiyyar mashigin teku ta Guinea tana da wadatuwar man fetur, bisa gididdigar da aka yi, yawan man fetur da aka gano a kasashen da ke shiyyar nan, wato kasar Nijerya da kasar Cameron da kasar Eq-Guinea da kasar Gabon da kasar Kongo Brazzaville da kuma kasar Angola ya kai ganguna biliyan 50. A shekarar 2001, man fetur da aka gano a duk duniya ya kai ganguna biliyan 8, inda ganguna biliyan 7 suna cikin shiyyar mashigin teku ta Guinea ta Afrika.
Manazarta sun nuna cewa, ko ta fanin sayen man fetur ko ta fanin samar da man fetur kai tsaye, kasar Sin da kasashen Afrika suna da kyakkyawar sakamako kan hadin kan man fetur. (Bilkisu)
|