Ran 14 ga watan nan, a birnin N'Djamena, hedkwatar kasar Chadi, wakilin gwamnatin kasar Sudan da na dakarun masu adawa da gwamnati mai suna "kungiyar gyare gyare da raya kasa" da ke shiyyar Darfur sun fara yin shawarwari.
An yi wannan shwarwari ne bisa kokarin da gwamnatin kasar Chadi ta yi wajen sulhuntawa. Bangarorin 2 da suke shwarwari za su mai da hankulansu kan yadda za a daidaita matsalar Darfur.
A farkon wannan shekara, kungiyar gyare gyare da raya kasa ta balle kanta daga wata kungiyar dakaru masu adawa da gwamnati mai suna "kungiyar neman samun adalci da daidaici". Sabo da kungiyar neman samun adalci da daidaici ta nuna kin yarda ga kungiyar gyare gyare da raya kasa kan shigowarta cikin shwarwarin neman daidaita matsalar Dardur na zagaye na 3 da ake yi a Nijeriya, shi ya sa, an canja wurin da gwamnatin kasar Sudan da kungiyar gyare gyare da raya kasa za su yi shawarwari zuwa Chadi.(Bello)
|