Ran 14 ga watan nan, babbar jam'iyyar adawa ta kasar Mozambique ta ce an aikata zamba a cikin babban zaben da aka yi a farkon wannan wata, don haka ta bukaci da a sake jefa kuri'a.
Ran 10 ga watan nan, Kungiyar Dagiya ta kasar Mozambique (RENAMO) , jam'iyyar adawa mafi girma ta kasar ta yi zargi cewa, Jam'iyyar 'Yanta da kasar Mozambique (FRELIMO) da ke kan karagar mulki ta yi magudi a cikin zaben. Shi ya sa tana bukatar sake jefa kuri'a a duk fadin kasa. Amma, kwamitin zabe na kasar ya ki yarda da bukatan.(Bello)
|