A ran 13 ga wata a nan birnin Beijing, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin Zhou Yongkang ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan kasar Sudan za ta iya yin kokari kan daidaita matsalar da take fama da ita yanzu da kanta, kuma za ta iya cimma burin raya tattalin arziki da sulhuntar siyasa.
Mr. Zhou ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da kungiyar wakilan kasar Sudan wadda ke karkashin jagorancin malam Awad Ahmed Al-Jaz, wato ministan makamashi da albarkatun halittu na kasar Sudan.
Mr. Zhou ya kuma bayyana farin cikinsa ga dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Sudan. Ban da wannan, Mr. Zhou ya tabbatar da sakamakon da kasashen nan biyu suka samu a fannoni daban-dabam.
Malam Al-Jaz ya kuma gode wa gwamnatin kasar Sin domin ta nuna goyon baya ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sudan a cikin dogon lokacin da ya gabata. Malam Al-Jaz ya kuma yi fatan lokacin da ake gaggauta ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar Sudan, za a iya bude sabbin fannonin hadin guiwa a tsakanin kasashen nan biyu. (Sanusi Chen)
|