A ran 10 ga wata, wani jami'in kawancen kasashen Afirka ya bayyana cewa, an jinkirtar da lokacin yin sabon zageyen shawarwarin shimfida zaman lafiya a shiyyar Darfur ta kasar Sudan da kwana 1. Bisa ajandar da aka tsara, a ran 10 ga wata ne ya kamata a kira wannan sabon zagayen shawarwarin.
Wannan jami'in kawancen kasashen Afirka ya ce, dalilin da ya sa aka jinkirtar da wannan lokaci shi ne wasu wakilan kungiyoyi 2 masu adawa da gwamnatin Sudan da wasu masu neman sulhu ba su isa birnin Abuja na kasar Nijeriya a cikin lokaci ba.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a gun zagayen nan, muhimmin abun da za a tattauna shi ne yadda za a samu hanyar siyasa ta daidaita hargitsin Darfur kuma za a yunkura wajen ingiza bangarorin daban-dabam da su kai ga daddale wata yarjejeniyar shimfida zaman lafiya kwata kwata a tskaninsu kafin karshen shekarar nan. (Sanusi Chen)
|