A ran 9 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Zhang Qiyue ta bayyana cewa, kasar Sin tana son ba da gudummawarta kamar yadda ya kamata wajen daidaita maganar Darfur ta kasar Sudan.
Madam Zhang ta ce, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan halin da ake ciki a shiyyar Darfur, ta kuma yi aiki da yawa domin sassautar rikicin da ake fama da shi a shiyyar. Ban da wannan, kasar Sin ta riga ta samar wa gwamnatin kasar Sudan taimakon jin kai, kuma ta sa kaimi ga gwamnatin kasar Sudan da ta yi hadin guiwa da kasashen duniya wajen daukar matakai masu amfani domin kyautata halin ayyukan bayar da agaji da zaman lafiya da ake ciki a shiyyar. (Sanusi Chen)
|