Ran 6 ga wata, bisa nan labarin daga kasar Kamaroon, an ce 'yan matan kasashen Afirka suna fuskantar babbar barzana ta ciwon sida, an ce takwas daga cikin duk 'yan mata guda goma masu dauke ne da kwayoyin cutar HIV 'yan matan Afirka ne. Yanzu, a kalla dai akwai 'yan matan Afirka masu dauke da cutar HIV wajen milliyan 13.
Labarin ya ce, abun mai jawo hankali na yaduwar ciwon sida a Afirka shi ne yawan 'yan mata masu dauke da cutar HIV suna karuwa da sauri, kuma 'yan mata sun zama masu saurin daukar ciwon cikin sauki.
|