|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2004-12-04 20:49:41
|
Shugaban kungiyar masu adawa da gwamnatin Sudan ya bayyana cewa, za a daddale yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin kungiyarsa da gwamnatin kasar a karshen shekarar nan
cri
Ran 3 ga wata, Mr John Garang, shugaban Kungiyar Kwatar 'Yancin Jama'ar Sudan wadda ke yin adawa da gwamnatin kasar ya bayyana a birnin Pretorina na kasar Afrika ta Kudu cewa, kungiyarsa ta dau niyyar aiwatar da kuduri mai lambar 1574 da Majalisar Dinkin Duniya ta tsaida, za ta daddale yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninta da gwamnatin Sudan daga duk fannoni kafin karshen shekarar nan.
Mr Garang ya yi wannan kalami ne bayan da aka yi shawarwar a tsakaninta da Mr Jacob Zuma, mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudu a wannan rana. A ran 6 ga wata, Mr Garang zai je Naibashe na kasar Kenya don yin shawarwarin sulhu a tsakaninsa da Mr Ali Osman Taha, mataimakin shugaba na farko na kasar Sudan. (Halilu)
|
|
|