Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-12-02 17:36:46    
Wata muhimmiyar ziyara wadda ta inganta dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

Daga ran 29 ga watan Oktoba zawa ran 8 ga watan Nuwamba na wannan shekara, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr.Wu Bangguo ya kai ziyarar aiki ga kasashen Kenya, da Zimbabuwe, da Zambia da kuma Nijeriya bisa gayyatar da aka yi masa.

Wannan ziyarar da Mr.Wu ya kai wa kasashe 4 na Afirka wani muhimmin aikin diplomasiyya ne daban da wani kusa a kasar Sin ya yi a Afirka, bayan ziyarce-ziyarcen da shugaba Hu Jintao da firayin minista Wen Jiabao da kuma mataimakin shugaban kasar Mr.Zeng Qinghong suka kai wa Afirka a karshen shekarar bara, wadda take da muhimmanci sosai ga inganta dangantakar zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. A lokacin ziyarar, Mr.Wu ya yi shawarwari da shugabannin kasashen nan 4 da shugabannin majalisunsu bi da bi, inda suka yi musanyar ra'ayoyi a kan dangantakar da ke tsakanin kasashen nan da hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kuma sauran batutuwa masu jawo hankulansu, kuma sun samu ra'ayi daya a fannoni da dama.

Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma, kuma Afirka nahiya ce inda aka fi samun kasashe masu tasowa. Mr.Wu ya yi ta jaddada cewa, bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka, tushen manufofin diplomasiyya na kasar sin ne, kuma manufa ce da kasar Sin ke tsayawa tsayin daka a kai. Makasudin wannan ziyarar da ya yi shi ne a kara bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da ksashen Afirka. Mr.Wu ya kuma nuna musu godiya sabo da goyon bayan da wadannan kasashe 4 suke bai wa kasar Sin har kullum a kan maganar Taiwan da ta Tibet da kuma hakkin bil Adam na kasar Sin, ya jaddada cewa, wannan tushen siyasa ne na dangantakar bangarorin biyu. Kasashen nan 4 su ma sun nuna yabo ga kokarin da kasar Sin ke yi wajen neman raya dangantakar da ke tsakaninta da su, kuma sun sake bayyana cewa, za su ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, ko a nan gaba ma, ba za su canja wannan matsayin da suke dauka ba. Dukan bangarorin biyu suna ganin cewa, dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, ya samar da wani dandali ga kasar Sin da kasashen Afirka inda za su yi shawarwari da kuma hadin gwiwa. Kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, buri ne na dukan jama'ar kasar Sin da ta Afirka, wanda ya dace da moriyar bangarorin biyu, kuma zai amfana wa bunkasuwarsu tare.

Ingiza yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da kasashen nan 4 shi ma babban makasudin wannan ziyarar da Mr.Wu ya yi ne, wanda kuma ya jawo hankulan shugabannin wadannan kasashe 4. Mr.Wu ya yi bayani a kan ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umm tun bayan da ta bude kofa ga duniya da yin gyare-gyare a gida, ya jaddada cewa, bunkasuwar Sin ta samar da zarafi ga yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana so ta ingiza hadin gwiwarta da kasashen Afirka a fannonin makamashi da kayayyaki da ayyukan noma da na kira bisa ka'idar moriyar juna, kuma su nemi sabuwar hanyar yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki. Mr.Wu y ci gaba da cewa, Kasar Sin za ta karfafa gwiwar kamfanoni masu karfi da su tafi kasashen nan 4 don zuba jari, kuma tana son a shigar da kayayyaki masu kyau daga kasashen nan 4, haka kuma, tana fatan kasashen nan 4 za su samar da kyawawan sharudda ga kamfanonin kasar Sin. Shugabannin kasashen 4 sun amsa da cewa, karfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da ciniki muhimmin kashi ne na hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, suna so a fadada fannoni da kuma hanyoyin yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za a samu nasarori tare.

Mr.Wu ya bayyana cewa, yin cudanya tsakanin majalisun kasashe daban daban muhimmin kashi ne na inganta dangantakar da ke tsakaninsu. Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kuma majalisun wadannan kasashe 4 dukansu sun taka muhimmiyar rawa cikin harkokin siyasa na kasarsu, kuma suna daukar nauyin karfafa diplomasiyya da kafa dokoki. Ya ce, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta mai da muhimmanci sosai a kan mu'amalar da ke tsakaninta da majalisun kasashen nan 4, kuma tana so ta yi kokari tare da majalisun nan, don a kara yin cudanya tsakanin shugabanni da kwamitocin musamman da kuma kungiyoyin sada zumunta na bangarorin biyu a fannoni daban daban, kuma a kara yin musanyar ra'ayoyi a kan kafa dokoki da sa ido a kan yadda ake aiwatar da dokoki. Shugabannin majalisun kasashen nan 4 sun yarda da wannan shawarar da Mr.Wu ya bayar sosai, su ma sun bayyana burinsu na kara yin mu'amala da hadin gwiwa da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

A karshe dai, Mr.Wu ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka, ciki har da kasashen nan 4, suna da moriya daya da kuma tushen yin hadin gwiwa cikin harkokin duniya, haka kuma suna da ra'ayi daya ko kusan daya a kan halin da ake ciki a duniya. Ya sake bayyana cewa, kasar sin za ta ci gaba da goyon bayan daidaitaccen ra'ayi da bukata na kasashe masu tasowa da suka hada da kasashen Afirka, kuma za ta karfafa hadin kai da kuma hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, haka kuma za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da kasashen Afirka suke yi wajen daidaita rikicin shiyya shiyya da bunkasa tattalin arziki. Kuma gwamnatin kasar Sin tana so ta daidaita matsayinta tare da kasashen Afirka cikin harkokin duniya, don su kiyaye moriyar kasashe masu tasowa tare. Kasashen nan 4 sun kuma nuna babban yabo ga manufar diplomasiyya ta shimfida zaman lafiya kuma ba tare da tsangwama ba wadda kasar Sin ke aiwatarwa, kuma suna fatan kasar Sin za ta kara sa muhimmanci kan rawar da take takawa cikin harkokin duniya a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma.

Ko da yake Mr.Wu bai dade da yin wannan ziyara ba, amma an sami babbar nasarar ziyarar. Mun gaskata cewa, bisa kokarin da bangarorin biyu suke yi tare, za a iya kara samun ci gaba a fannin karfafa hadin gwiwa da kuma dangantakar da ke tsakaninsu.(Lubabatu)